
Shirin Duniyar wasanni na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankalin kan dambarwar rikicin shugabancin da ya dabaibaye hukumar kula da gasar Polo a Najeriya, Ayi saurare Lafiya.
Feb 28, 2022
11 min

Shirin 'Duniyar Wasanni' ya yi nazari a kan yadda ta kaya a gasar zakarun nahiyar Turai, zagayen kungiyoyi 16.
Feb 21, 2022
9 min

Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako, ya halarci gasar gudun fanfalaki na 'Lagos Marathon' da aka gudanar a birnin legas da ke Najeriya. Cikin wadanda suka shiga wannan tsere, har da gwamnan jihar ta lEGAS, babajide Sanwo-Olu.
Feb 14, 2022
10 min

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da AbduRahman Gambo Ahmad ya tattauna akan nasarar da kasar Senegal ta samu wajen lashe kofin gasar kwallon kafa ta kasashen Afirka da Kamaru ta karbi bakunci.
Feb 7, 2022
9 min

Hukumar kwallon kafar Afrika ta sanar da dage haramci da ta yi na soke wasanni a filin wasa na Olembe biyo bayan mutuwar mutane 8 da aka samu ranar litinin 24 ga watan janairu 2022.
Jan 31, 2022
8 min

Shirin Duniyar Wasanni tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali kan gasar cin kofin Afrika da aka fara gudanarwa jiya lahadi a Kamaru, gasar a wannan karon na matsayin karo na 33 tun bayan farowa zuwa yanzu.
Jan 10, 2022
10 min

Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yada zango ne a garin Jos da ke jihar Filato ta Najeriya, inda aka kammala wasannin gasar kwallon dawaki da aka fi sani da Polo a Turance, gasar da ta samu halartar baki daga ciki da wajen Najeriya. Bashir Ibrahim Idris ya halarci gasar ta tsawon mako guda. Ku latsa alamar sautin domin sauraren cikakken shirin da ya hada.
Jan 3, 2022
9 min

Shirin Duniyar wasanni na wannan mako tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya mayar da hankali kan shirin tunkarar gasar cin kofin Afrika da za ta gudana a Kamaru da kuma jita-jitar da ke nuna cewa da yiwuwar kungiyoyi su hana 'yan wasan nahiyar halartar gasar.
Dec 27, 2021
10 min

Hulumar kwallon kafar Najeriya NFF ta sallami Gernot Rhor mai horar da kungiyar kwallon kafar Super Eagles.
Sallamar dake zuwa a wani lokaci da ya kasa kawo sauyi a tafiyar kungiyar ga baki daya.
a cikin shirin Abdurahaman Gambo Ahmad ya ji ta bakin ma'abuta kwallon kafa da kuma irin fatan su bayan nadin sabon mai horar da Super Eagles a cikin shirin Duniyar wasanni.
Dec 20, 2021
9 min
Load more
