
A cikin shirin kasuwa. a kai miki dole,Bashir Ibrahim idris ya duba halin da ake ciki a Najeriya musaman bayan da wani bincike ya nuna cewa matsalar tsaro ta sa yan kasuwa kaura daga yankunan su zuwa kasashen waje.
A cikin shirin za ku ta yada binciken ya nuna cewa jihar Gombe ce sahun gaba inda da dama daga cikin yan kasuwa a jihar suka kaura.
Aug 11, 2021
10 min

Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan mako ya maida hankali ne dangane da shirin gwamnatin Najeriya na tallafawa manoma da kuma kananan sana’o’i. Shirin wanda Babban Bankin Najeriya CBN ya kirkirir karamin bankin tsimi da tanadi na musamman da akayi wa suna da NIRSAL dake tallafawa manoma da kananan ‘yan kasuwa basuka maras kudin ruwa cikin sauki, batare da jingina ba, kamar yadda aka saba a wasu bankunan kasuwanci.
Jul 14, 2021
10 min

Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba, a yau ya mayar da hankali kan tsadar rayuwa da kuma tashin farashin kayaki a kusan ilahirin sassan Duniya, ko da ya ke lamarin ya tsananta a Najeriya kasar da alkaluma ke nuna yadda ake samun karuwar matalauta a kowacce rana.
Jul 7, 2021
10 min

Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' ya tattaunawa ne dangane da matsaloli ko asarar da matakin kasar Saudiya da hana aikin hajjin bana ya janyo, inda shirin ya yada zango jamhuriyar Nijar.
Jun 30, 2021
10 min

Shirin Kasuwa akai miki dole na wannan makon tare da Ahmed Abba ya mayar da hankali kan matakin kasar Saudiya na hana mahajjata aiwatar da aikin hajjin bana, matakin da ya haddasawa kamfanoni da dama asarar miliyoyin kudade. Ayi saurare Lafiya.
Jun 24, 2021
10 min

Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole' na wannan mako tare da Ahmed Abba ya maida hankali ne, dagane yadda takura da fulani makiyaya ke fuskanta a kudancin Najeriya ke shafar harkokin kiwo da safarar dabbobi daga arewaci zuwa kudancin kasar.
Jun 16, 2021
10 min

Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya yi nazari kan muhimman kanana da matsakaitan masana'antu ga tattalin arzikin Najeriya, dai dai lokacin da karancin lantarki ke taka muhimmiyar rawa wajen durkushewarsu. A yi saurare lafiya.
Jun 9, 2021
10 min

Shirin Kasuwa a kai miki dole na wannan makon yayi nazari ne kan halin da 'yan kasuwa suka shiga na cigaba da akasinsa sakamakon tasirin rufe iyakokin da Najeriya tayi tsakaninta da makwaftanta.
Jun 3, 2021
9 min

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan mako tare da Ahmed Abba ya duba batun musabbabin tsadar Siminti da kuma karuwar bukatarsa a Tarayyar Najeriya duk kuwa da matsin tattalin arziki da ake fama da shi, saboda matsalolin tsaro da annobar korona.
May 26, 2021
10 min

Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba kasuwar musayar kudin kasa da kasa a Najeriya inda kudin kasar na Naira ke cigaba da faduwa, yayin da kudaden kasashe ketare musamman Dallar Amurka, ke tashin goron-zabi. Menene tasirin wannan hawa-hawan farashin na Dalla ga tattalin arzikin Najeriya kuma ina mafita? wadandan sune abin da shirin ya yi nazari akai.
May 19, 2021
9 min
Load more
