Muhallinka Rayuwarka
Muhallinka Rayuwarka
RFI Hausa
Wayar da kan jama’a da ilmantar da su, game da sha’anin da ya shafi Noma da muhalli da canjin yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).
Halin da madatsun ruwa a jihohin Kano da Jigawa ke ciki kashi na 3
A wannan shirin za mu ƙarƙare jerin shirye-shiryen da muka fara kawo muku akan halin da madatsun ruwa ke ciki  jihohin Kano da Jigawa a Tarayyar Najeriya, da kuma yadda ya haan  ya shaf harkar noman rani da su, da kuma halin da ya jefa manoman da masunta, musamman ta fannin tattalin arzikinsu.
Jun 21, 2025
20 min
Taron ƙasa da ƙasa ƙan nazarin ƙasar noma da kiwo a jihar Kano
Cibiyar nazarin da bincike kan ƙasar noma ta jam'iar Bayero a jihar Kano dake Najeriya ce ta shirya taron da ya hada ƙasashe da masana da suka yi duba a kai. Taron karo na biyar ya baiwa masana damar nazari don lalubo hanyoyin magance matsaloli da suka hadabi wannan sashe da ya hada da noma da kiwo a Sahel da wasu ƙasashen.
May 24, 2025
20 min
Halin da madatsun ruwa da ke jihohin Jigawa da Kano ke ciki?
A wannan makon, shirin zai yi duba ne kan halin da madatsun ruwa da ke jihohin Jigawa da Kano ke ciki, da irin amfanuwa ko akasi da  masu cin moriyar su da suka haɗa da manoma da masunta da sauran al’ummmar yankunan ke yi da su.
May 18, 2025
19 min
Hobbasa na hukumomin Zinder wajen samar da yanayi mai ƙyau na noman shinkafa
Shirin  namu na yau zai mayar da hankali ne akan yadda mahukunta a jihar Damagaram ko Zinder ta Jamhuriyar Nijar suka yi hobbasa wajen samar da yanayi mai ƙyau na noman shinkafa ga manoman da suka bada himma  a bara, suka kuma ga amfaninta.
May 10, 2025
19 min
Manoman albasa sun tafka hasara a Nijar saboda rashin dacen iri
Shirin Muhalllinka Rayuwarka’ ya yada zango ne a jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar, inda ɗimbin manoman albasa suka shiga halin ‘ni ƴasu’ sakamakon yadda ƙaddara ta sa suka yi kiciɓis  da mugun irin albasa, lamarin da ya sa suka tafka asara.
May 6, 2025
19 min
Jigawa ta yi haɗin gwiwa da Saudiyya don haɓaka noman dabino
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan hadin gwiwa da Gwamnatin jihar Jigawa ta yi da wani babban kamfanin samar da dabino na kasar Saudiyya da kuma wani kamfanin ƙwararru da bunkasa harkokin noma na Najeriya. Babbar manufar wannan haɗin gwiwar ita ce bunƙasa noman dabino a jihar, ta hanyar bullo da dabarun noma na zamani, da musayar fasahohi, da kuma samar da jarin noma.
Apr 26, 2025
20 min
Yadda karye farashin kayan abinci zai yi tasiri akan noman bana
A yau shirin zai yi nazari ne akan yadda karyewar farashin kayan abinci zai yi tasiri akan noman  bana, sakamakon zargin da ake cewa gwamnatin ƙasar ta shigar da kayan abinci daga waje, wadanda ke gogayya da waɗanda manoman cikin gida suka noma. A shirin da ya gabata, mun kawo kukan da manoma ke yi akan wanna al’amari, inda suke cewa gwamnati ba ta yi wani abu a game da kayayyakin aikin gona da suke saya da tsada. A yau shirin zai duba irin tasirin da hakan zai yi da noman bana.
Mar 29, 2025
20 min
Manoma sun koka akan matakan gwamnatin Najeriya na karya farashin abinci
Manoma a Najeriya na cigaba da kokawa dangane da matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na karya farashin kayan gona a daidai lokacin da ƙasar ke ƙokarin samar da wadatar abinci.
Mar 26, 2025
20 min
Yadda ƙarancin ruwa ke mummunan tasiri akan aikin noma da samar da abinci
Shirin ya yi duba kan yadda matsalar ta ƙaracin ruwa ke haifar da tasgaro a fannin noma don samar da wadatar abinci, inda mu ka ji daga manoma musamman na rani a Najeriya kan irin kalubale da su ke fuskanta na rashin samun wadataccen ruwa a gonakinsu, a daidai lokacin da ƙasar ta yi watsi da batun gyara galibin madatsun ruwa da ake da su ballantana ma a kai ga batun gina sabbi.
Mar 17, 2025
19 min
Yadda masu aiki a cikin teku ke rayuwa har ma da yadda za a yi amfani da teku
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wanan makon tareda Micheal Kuduson wanda  kashi  na uku ne ya dora akan kashi na biyu wanda ya gabata a makon jiya. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata shirin ya mayar da hankali ne kacokam akan yadda masu aiki a cikin teku ke rayuwa har ma da yadda za a yi amfani da teku, tafki, rafi ko kogi domin gudanar da harkokin noma da kuma kyautatawar muhalli.
Mar 9, 2025
20 min
Load more