
Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris, ya tattauna ne akan dokar kare hakkokin yara kanana, wadda bayan shafe shekaru da sanya hannu kan amincewa da ita da majalisar dokokin Najeriya ta yi jihohi da dama suka gaza aiwatar da dokar.
Dec 7, 2021
10 min

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari ne game da matakan da gwamnatin jihar Yobe ta dauka na bunkasa ilimi a jihar bayan fama da rikicin Boko Haram
Nov 30, 2021
9 min

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya leka Jamhuriyar Nijar ne domin yin nazari game da wani tsari na korar daliban da suka fadi jarawaba sau biyu. Amma a yanzu an samu wata badakala ta cuwa-cuwar kera takardu na jabu domin sake mayar ire-iren wadannan daliban wata makaranta ta daban.
Nov 23, 2021
10 min

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya tattauna ne game da sabuwar jaridar Tabarau wadda ake rubuta cikin ajami domin bunkasa yaduwar ilimi tsakanin al'ummar Hausawa musamman makaranta Al-Kur'ani mai girma.
Nov 16, 2021
11 min

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda yake tattaunawa game da wani taro da aka gudanar a jami'ar Bayero ta Kano da ke Najeriya kan inganta fassarar labarai a harsunan cikin gida.
Nov 9, 2021
10 min

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya halarci wani taron masana ne a Jami'ar Bayero ta Kano wanda ya yi nazari kan inganta fassara a harsunan gida.
Nov 2, 2021
10 min

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris ya dora kan shirin makon jiya game da fasahar da wani matashi ya samar mai yanayi da dandalin sada zumunta na Watsapp wanda ya yiwa suna da Tabarau, da ke zuwa dai dai lokacin da aka samu daukewar kafofin sada zumunta na Watsapp, Facebook da kuma Instagram.
Oct 19, 2021
9 min

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Bashir Ibrahim Idris ya mayar da hankali kan daukewar kafofin sada zumunta na Watsapp, Facebook da kuma Instagram dama yadda wani matashi ya kera wata manhaja da ke kamceceniya da Watsapp.
Oct 12, 2021
10 min

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim ya tattauna ne kan shirin gwamnatin jihar Borno ta Najeriya na ilmantar da marayu a daidai lokacin da Hukumar UNICEF ta ce, sama da yara miliyan 10 ne ke zaune a gida ba tare da zuwa makaranta ba a Najeriya, kuma akasarinsu na rayuwa ne a yankin arewacin kasar.
Sep 21, 2021
9 min

A cikin shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' Bashir Ibrahim Idris ya kawo yada hukumar sadarwar Najeriya ta tashi tsaye don magance dukkannin matsalolin da ke addabar bangaren.
Sep 14, 2021
10 min
Load more
